Dattijuwar da ke wayar da kan jama'a kan muhimmancin jima'i ga tsofaffi

Bayanan bidiyo, Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Dattijuwar da ke wayar da kan jama'a kan muhimmancin jima'i ga tsofaffi

Seema Anand masaniya ce kan ilimin jima'i da tatsuniyoyi wadda babban burinta shi ne ta kawar da camfe-camfen da wasu ke yi cewa tsofaffi ba sa jin dadin jima'i kuma yin sa yana da hatsari a gare su.

Ta kwashe kusan shekaru ashirin tana gudanar da bincike da yin nazari game da inzali a hikayoyin kasar Indiya inda ta rubuta littattafai da dama game da jin dadin jima'i.

Sai dai ta ce bayan ta bude shafin sada zumunta, ta gano cewa wasu suna ganin yin magana a kan batun haramun ne inda aka rika yin barazanar kashe ta.