'APC sa'a ta yi aka sake zaɓen ta a 2019'
Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawal ya ƙalubalanci masu bayyana majalisar dokokin ƙasar a matsayin ƴan amshin shata sakamakon yadda suke sahale wa ɓangaren zartarwa aiwatar da al'amuran cigaban ƙasa.
"Sun fi son a rinƙa yin ihu da zage-zage shi ne sai jama'a su ce majalisa na aiki.
Lokacin da muka yi rigingimu da 2015 zuwa 2019, a faɗa min ribar da aka samu ko kuma a faɗa min irin aikin da gwamnati ta yi saboda rigima.
Ya ce irin waɗannan rigingimu ne suka sa gwamnatin jam'iyyar APC kusan ba ta yi komai ba, a shekaru hudunta na farko.
"APC sa'a ma ta yi aka sake zaɓen ta a 2019," in ji shugaban majalisar dattijan zango na tara da ta shuɗe.
A cewarsa, saboda a shekaru huɗun ba wani aiki da aka yi saboda rigima (tsakanin majalisa da ɓangaren zartarwa).
Ya ce akwai abin da mutane ba sa gani.
Gwamnatin shugaba Buhari wadda APC ce, mun nemi a kafa kwamitin wanda zai hada da shugaban kasar da kansa amma sai ka ga idan ana tattaunawa an kasa cimma matsaya." In ji Sanata Lawal Ahmed.
Da yake magana dangane da rawar da majalisar ta taka wajen tabbatar da mulkin dimokraɗiyya, sanatan ya ce majalisar dokokin ƙasar ce ta sa Najeriya a turbar dimokradiyya duk da dai akwai wasu 'yan kurakurai.
"A lokacin da na zo majalisa a shekarar 1999, an yi shugaban da ke da tunanin bai ma kamata majalisa ta zama mai cin gashin kanta ba. Gaskiya majalisa ta samu komabaya sosai daga 1999 zuwa 2003 saboda kuɗin da za mu sayi kayan aiki hatta takardu sai ɓangaren zartarwa ya ba mu.
"An hana mu aiki yadda ya kamata. Sai ka ga ɓangaren zartaswa ba ta cika son mai cizo da yawa ba. Amma yanzu abubuwan sun kau. Amma yanzu duk wannan ya kau"
Ya ƙara da cewa har yanzu akwai matsalolin da tsarin dimokraɗiyyar ke fuskanta "domin har yanzu akwai ƙalubale a zaɓukan ƙananan hukumomi. Kuma majalisun dokoki na tarayya da jiha da ma sauran jama'a suna da rawar da za su taka."
To sai dai ya ce dimkoraɗiyyar ta samu cigaba a tsawon shekaru 25.
"Gaskiya babban abin da aka samu shi ne kasancewar an samu shekara 25 ɗin nan ba tare da dakatarwa (juyin mulki) ba. Sannan idan ka dubi irin yadda jam'iyyar adawa ta karɓe mulki daga hannun jam'iyya mai mulki a 2015. "



