Manomin da ke neman buhun taki ɗaya domin amfani a gonakinsa huɗu a Kano
Manomin da ke neman buhun taki ɗaya domin amfani a gonakinsa huɗu a Kano
Wani ƙaramin manomi, Yahuza Yahya a jihar Kano ya ce zai sayi takin zamani buhu ɗaya a bana don amfani a gonakinsa huɗu, idan ya gaza samun tallafi daga hukumomi.
Manoma a damunar bana suna kokawa game da tsadar taki da iri da maganin feshi, daidai lokacin da hauhawar farashin abinci ta kai wani mataki.
Mallam Yahuza Yahya ya ce ya samu labari gwamnati a jihar Kano ta ƙaddamar da rabon takin zamani kuma yana sa ran zai samu, amma idan bai samu ba dole ne ya lale naira 40,000 ya sayi taki ɗaya.



