Ɗan Najeriya da ke magana da manyan yarukan ƙasar
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalan da ke ci wa Najeriya tuwo a ƙwarya har a wannan lokaci da ta cika shekara 65 da samun 'yancin kai daga Birtaniya, shi ne ƙiyayya da zargin yi wa juna manaƙisa a tsakanin ƙabilun ƙasar.
Wannan na kai wa ga tashin rikicin ƙabilanci a lokuta daban-daban, abin da kan janyo zubar da jini da kashe-kashe.
Rikice-rikice da zargin shirya wa juna manaƙisa, sun ta'azzara rarrabuwar kai da rashin yarda da juna tsakanin ƙabilu daban-daban tsawon lokaci.
Wannan ne ya sa fitaccen mai shirye-shiryen nan a kafafen sada zumunta musamman wajen fito da ƴan Najeriya masu basirar koyon harsuna da dama mai suna Adedeji Udulisi, wanda ɗan ƙabilar Yarabawa ne, yake ƙoƙarin haɗa kan ƴan ƙasar ta hanyar harasa.

An haifi Adedeji ne a jihar Delta, inda ya iya Turancin Buroka kafin daga bisani mahaifan nasa su koma Sokoto inda kuma a can ya koyi harshen Hausa.
Daga aiki ya komar da iyayen nasa jihar Imo inda a nan ne ya ji harshen Igbo.
Mutumin mai baiwar iya harasa da dama ya ce ya yi jami'ar a jihar Ogun wadda ita ce jiharsa ta asali, inda kuma a nan ne ya samu damar lakantar harshen Yarubanci.
Bugu da kari, baya ga lakantar harasan Najeriya manya guda uku da suka hada da Hausa da Yarabanci da Igbo da kuma Turancin Buroka, Adedeji yana kuma fahimtar harshen Faransanci ƙari a kan Turanci.



