Da a kashe mutum ɗaya a Kaduna, gara na yi sulhu da ƴanfashi - Uba Sani

Bayanan bidiyo, Da a kashe mutum ɗaya a Kaduna, gara na yi sulhu da ƴanfashi - Uba Sani
Da a kashe mutum ɗaya a Kaduna, gara na yi sulhu da ƴanfashi - Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana wa BBC dalilan da suka sanya gwamnatinsa ta amince ta yi sulhu da ƴanfashin daji a jihar yayin da jihohin da ke maƙwaftaka suka yi watsi da irin wannan tsari.

A cikin watan da ya gabata ne bayanai suka ɓulla kan sasancin da gwamnatin jihar ta yi da ƴanfashin waɗanda suka daɗe suna addabar yankunan jihar.

Lamarin da al'ummar yankunan da rashin tsaro ya fi shafa, kamar Birnin Gwari da Giwa da ƙauyukan ƙaramar hukumar Igabi suka ce ya kawo musu kwanciyar hankali.