Matar da aure ya sa ta nemo mahaifinta da ba ta taba sani ba

Bayanan bidiyo, Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Matar da aure ya sa ta nemo mahaifinta da ba ta taba sani ba

Sashen binciken kwakwaf na BBC ya bibiyi tafiyar da wata ƴar jarida Namukabo Werungah, ta yi, wacce ba ta san mahaifinta ba, kuma ta yanke shawarar neman inda yake.

Ba ta sani ba, ko yana da rai ko ba shi da rai, sai dai yadda aurenta ke ci gaba da ƙaratowa, ta ga cewa lokaci ya yi da za ta san tarihinta.

Shin za ta iya gano inda wanda ya kamata ta kira da sunan mahaifi yake kuwa?

Kuma idan har burinta ya cika, ta gano shi, zai so ta a rayuwarsa kuwa?