Gane Mini Hanya: Ina PDP, amma zan yi aiki da haɗakar kayar da Tinubu - Sule Lamiɗo
Lokacin karatu: Minti 1
Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo ya ce yadda ya san halin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan cika burin da ya sa a gaba, na cikin abubuwan da suka ƙara masa ƙaimi wajen shiga sabuwar haɗakar ƴan hamayya ta ADC.
Ya ce ya amince ya yi aiki da haɗakar ne a wani yunƙuri na kawar da gwamnatin Tinubun a babban zaɓen ƙasar mai zuwa.
Sai dai a ɓangare guda Sule Lamido, ya ce ba zai fita daga jam'iyyarsa ta PDP ba - wani salo da ke ƙoƙarin zamewa ruwan dare a siyasar Najeriyar a baya-bayan nan.
A zantawarsa da wakilinmu na Kano, Zahraddeen Lawan cikin filinmu na Gane Mini Hanya a wannan mako, tsohon gwamnan Jigawa ya fara ne da yin waiwaye kan abin da yake gani shi ne mafari na halin da siyasar Nijeriya ta samu kanta ciki.








