Yadda ake haɗa wayar caji ta USB a Kano

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Yadda ake haɗa wayar caji ta USB a Kano

Sharfuddeen Sadiq wani matashi ne a jihar Kano mai haɗa wayoyin caji na wayoyin salula kamar Iphone da Android, kuma suna samun karɓuwa a Najeriya da wasu ƙasashen waje.

Matashin ya ce burinsa shi ne Najeriya ta rage shigo da kaya daga ƙasashen ƙetare, da kuma samar wa matasa aiki inda a halin yanzu yana da ma'aikata fiye da 20.