Matashin ma'aikacin banki da ke wakokin soyayya a Kano

Matashin ma'aikacin banki da ke wakokin soyayya a Kano

Akwai dumbin matasa masu zalaka da basira musamman ta kirkirar wakoki a fannonin rayuwa masu yawa, a baya-bayan nan har a bangaren aikin banki.

Ba kasafai dai ake ganin ma'aikatan banki suna hada sana'arsu da wani aikin na daban ba, amma yanzu matasa kamar wani Ja'afar Usman a Kano, sun fara fitowa, suna nuna cewa aikin a bangaren harkokin kudi ba zai hada su ci gaba da zakulo baiwar da Allah ya yi musu ba.

Matashin dai yana rera wakoki irin na soyayya da na fadakarwa, inda ake gayyatarsa wuraren biki don cashewa.