Matashin da ya ɗura kasuwanni kusan 1000 a manhajar da ya ƙirƙiro
Harkokin kasuwanci da na tattalin arziƙi, suna ci gaba da haɓaka a faɗin duniya musamman albarkacin yaɗuwar fasahohin zamani da ke bai wa mutane damar yin saye da sayarwa ko da suna kwance daga gida.
Wata sabuwar manhaja mai suna acrossmart, na ɗaya daga cikin irin waɗannan fasahohi da wani matashi ya ƙago don bunƙasa kasuwanci a Najeriya.
Sa’id Sulaiman, ɗan shekara 30, ya ce ya ga buƙatar ƙirƙiro manhajar acrossmart ne lokacin da yake raka wani abokinsa zuwa kasuwanni a faɗin birnin Kano don haɗa kayan lefe.
A cewar, matashin wanda likitan fiɗa ne, manhajar za ta bai wa mutum damar saye ko sayar da haja kusan a ko'ina yake a faɗin Najeriya.
Ya ce ya kwashe tsawon shekara biyu yana bincike da tsare-tsare kafin ya cimma burinsa na ƙirƙiro manhajar.



