Hasumiyar da ta kare Katsina daga mayaƙa shekaru 500 da suka gabata

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
Hasumiyar da ta kare Katsina daga mayaƙa shekaru 500 da suka gabata

Labarin hasumayar Gobarau a tsakiyar birnin Katsina na komawa ga ƙarni na 15 lokacin Sarki Muhammad Korau wanda ya rayu tsakanin 1445 zuwa 1495 wanda kuma shi ne Sarki na farko na Musulunci.

Tarihi ya nuna cewa Malamin addinin Musulunci Sheikh Muhammad Abdulkarim Almaghili wanda aka haifa a ƙsar Algeria.

Sheikh Almaghili ya bayara da shawara ga Sarki Korau da ya gina hasumayar wadda ta zama masallacin Juma'a, yayin wata ziyara da ya kai birnin.

Baya ga yin kiran sallah da ake yi a kan hasumayar, ana amfani da ita domin gano idan mayaƙa sun tunkaro garin.

Ma'aikata:

Rahoto: Rabi'atu Kabir Runka

Bidiyo da tsarawa: Abba Auwalu