Yau za a fara yaƙin neman zaɓen 2027 a Najeriya

    • Marubuci, Muhammad Annur Muhammad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Larabar nan ne 19 ga watan Agusta 2026 za a fara yakin neman zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya a hukumance a Najeriya, kamar yadda hukumar zaben kasar INEC ta bayyana.

A bayananta hukumar ta ce, daga ranar jam'iyyu da 'yansiyasa za su fara yakin neman zaben har zuwa jajiberin ranar kada kuri'a - sa'a 24 kenan da za a gudanar da zaben na shekara mai zuwa - 2027.

A tattaunawarta da BBC, mai magana da yawun hukumar zaben ta Najeriya, Zainab Aminu Abubakar ta bayyana hakan:

''Kamar yadda dokar zabe ta 2026 ta tanadar, sashe na 94, sakin layi na biyu, ya bukaci jam'iyyun siyasa su fara yakin neman zabe na zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisu na tarayya, kwanaki 150 kafin ranar zabe.''

''Kuma duba da jadawalin zaben 2027 hukumar zaben ta ayyana yau 19 ga watan Agusta a kan ranar da za a fara wannan gangamin yakin neman zaben wadannan kujeru,'' in ji ta.

Za a yi zaben na shugaban kasa ne da 'yan majalisun tarayya - na dattawa da kuma na wakilai ranar 14 ga watan Janairun 2027, kamar yadda jadawalin hukumar zaben ya nuna.

Lokacin kamfe na gwamnoni da 'yan majalisun jiha

Shi kuwa yakin neman zaben gwamnoni da na majalisun jihohi za a fara shi ne ranar tara ga watan Satumba, 2026, kamar yadda jadawalin na INEC ya tabbatar.

Zaben gwamnonin da 'yan majalisun jihohi kuwa za a yi shi ne, ranar 6 ga watan Fabarairu na shekarar ta 2027.

Dokokin zabe sun kuma tanadi cewa dole ne a dakata da duk wani gangamin yakin neman zabe sa'o'a 24 kafin ranar zabe.

Dangane da abubuwan da ya kamata 'yan siyasar su kiyaye da su, kamar yadda doka ta tanada.

Zainab ta ce, babban abin da ya kamata su kiyaye da shi, shi ne yin yakin neman zabe ba tare da tashin hankali ba ko rigingimu da amfani da 'yanbanga ba.

Ta kara bayani da cewa: ''Kuma jam'iyyun siyasa da 'yan takara su kiyaye da amfani da kalamai na batanci ko cin zarafi ga wata jam'iyya ko dantakara ko kuma cin zarafi ga wani sashe na kasa ko wani addini.''

''Haka kuma doka ta hana yakin neman zabe a wurare na ibada. Domin wuararen ibada ba wuri ne da za a je ana yakin neman zabe ba, domin Najeriya kasa ce da ta kunshi addinai daban-daban da yaruka daban-daban.

''Idan aka ce za a rika bin layin addini ko kabila wajen yakin neman zabe to za a iya kawo barazana ga hadin kai da zaman lafiya da ake kokarin ganin an gina a kasar,'' in ji mai magana da yawun INEC din.

Abubuwan da doka ta hana

Mai magana da yawan INEC din ta kuma ce doka ta hana jam'iyyu biyu ko fiye da haka su fito a rana daya a waje daya a lokaci daya kowace ta ce za ta yi yakin neman zabenta, domin za a iya samun tashin hankali.

''Shi ya sa doka ta tanadi cewa kowace jam'iyya ta sanar da jami'an tsaro rana da lokaci da wuri da za ta gudanar da yakin neman zabenta, saboda su wadannan jami'an tsaro za su iya tsara yadda za a kaucewa matsala a ce wannan jam'iyya ta fito waccan ma ta fito ba a lokaci daya,'' a cewarta.

Shirin da jam'iyya mai mulki ta yi na kamfe

Yayin da lokacin gudanar da yakin neman zaben ya fara a hukumance a ranar Laraba, hankula sun karkata kan yadda jam'iyyar APC mai mulki za ta yi amfani da babban tsarinta na siyasa a fadin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya - Abuja domin gudanar da yakin neman zaben.

Jam'iyyar mai mulkin Najeriya ta ce za ta bayyana cikakken shirinta na yakin neman zaben 2027 nan ba da jimawa ba.

Sai dai ta ce ba za ta yi gaggawar fara tarukan gangami ba da zarar lokacin yakin neman zabe ya fara.

Sakataren yada labaranta, Barrista Felix Morka, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, ranar Litinin, bayan wani taron kusan sa'a uku da kwamitin zartarwa na jam'iyyar ya gudanar a hedikwatarta da ke Abuja.

Morka ya ce duk da cewa INEC ta kayyade ranar 19 ga Agusta a matsayin ranar fara kamfe, babu wata doka da ta tilasta wa jam'iyyu fara gangami a ranar.

Ya ce: "19 ga Agusta ita ce ranar da INEC ta ware domin dukkan jam'iyyu su fara yakin neman zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya. Amma babu wata doka da ta ce dole ne mu fara a wannan rana. Abin da doka ta haramta shi ne fara kamfe kafin wannan rana."

Ya kara da cewa APC na ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki da 'yan takararta domin tsara wani tsari na yakin neman zabe da zai kasance cikin daidaito a fadin kasar, maimakon yin gaggawar fara gangami.

Abubuwan da za su dauki hankali a kamfe

Wasu masu lura da al'amuran siyasar kasar ta Najeriya na ganin matsalolin tsaro da tsadar rayuwa za su kasance cikin manyan batutuwan da za su mamaye yakin neman zaben na 2027.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman sake komawa mulki, sai dai rahotanni na nuna cewa farin jininsa ya ragu a tsakanin matasa, yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.

Daga cikin manyan 'yan takarar hamayya da ake sa ran za su fafata akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, na jam'iyyar ADC.

Sai kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, wanda ya yi wa jam'iyyar Labour takarar shugaban kasa a zaben 2023 Peter Obi, wanda a wannan karon zai yi wa jam'iyyar NDC takara.

Jam'iyyun hamayya dai na fuskantar rarrabuwar kai, lamarin da wasu masu sharhi ke ganin zai iya yin tasiri kan karfinsu a zaben.

A wani rahoto, Bankin Duniya ya ce fiye da rabin al'ummar Najeriya a yanzu na rayuwa ne a cikin matsanancin talauci.

Masu sa ido na ganin yadda 'yan takara za su tunkari matsalolin tsaro, tattalin arziki da walwalar jama'a na daga cikin abubuwan da za su taka muhimmiyar rawa wajen rinjayar masu kada kuri'a.