'Siyasar ubangida na tauye wa matasa ɗumbin dama a Najeriya'
'Siyasar ubangida na tauye wa matasa ɗumbin dama a Najeriya'
Tsohon shugaban matasa na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Ismail Ahmed, ya ce siyasar ubangida ce abin da ya fi daƙile matasa wajen shiga a dama da su a siyasar ƙasar.
Ismail wanda lauya ne, ya ce akwai ƙalubale mai girma ga matasan saboda "akwai maganar kuɗi sosai" a siyasar Najeriya.
Mun ji ra'ayin Barista Ismail ne albarkacin cika shekara 25 da komawar Najeriya kan turbar dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba.



