Manhajar da ke taimakawa wajen magance safarar damisa ba bisa ka'ida ba

Bayanan bidiyo, Manhajar da ke taimakawa wajen magance safarar damisa ba bisa ka'ida ba
Manhajar da ke taimakawa wajen magance safarar damisa ba bisa ka'ida ba

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Safarar da ake yi ta damisoshi ta haramtacciyar hanya tana barazana ga yunkurin masu kare muhalli na kare dabbobin da ke fuskantar barazanar ƙarewa daga doron kasa.

Tana karfafa gwiwar masu kiwon damisa inda ake tilasta musu yin rayuwa cikin mawuyacin hali.

Hukumar kare muhalli ta the Environmental Investigation Agency (EIA) da masana kimiyya a Cibiyar Alan Turing suna fatan sabuwar manhajar da suka kirkira za ta taimaka wa jami'an tsaro bankaɗo masu safarar damisoshi.