Matashiyar da ke tuƙin motar Bolt a Kano

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Matashiyar da ke tuƙin motar Bolt a Kano

Maryam Abubakar AA ta ce ta fara sana'ar tuƙin mota ne saboda sana'ar da take yi, ta yi ƙasa.

Matashiyar 'yan asalin jihar Kano, ta kuma ce da farko ta fuskanci tarin ƙalubale kan wanna sana'a da take yi.

Maryam - wadda ke karatu a jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano - ta ce tun da farko Mahaifinta ya ce dole sai ta riƙa sanya hijabi a lokacin gudanar da sana'ar tata.

b