Matashin da yake hada sana'ar waka da ta gadi

Bayanan bidiyo, Mutumin da yake hada sana'ar waka da ta gadi
Matashin da yake hada sana'ar waka da ta gadi

Wani matashin mawaki a arewacin Najeriya ya ce yana hada sana'arsa ce da ta gadi domin fadada hanyoyin samun kudi.

Muhammad Musa Bello (MMB), dan asalin Jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya, ya shaida wa BBC cewa ya soma waka ne kusan shekaru 15 da suka gabata domin fadakar da al'umma, yana mai cewa "sannan kuma soyayya [ta sa ni yin waka]."

MMB, wanda ke yin wakoki da harsunan Hausa da Turanci, ya kara da cewa yana amfani da sana'arsa ta gadi ne wajen tallata wakokinsa.