'Jami'anmu 35,000 ne za su ba da tsaro yayin zaɓen gwamnan Edo'
'Jami'anmu 35,000 ne za su ba da tsaro yayin zaɓen gwamnan Edo'
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Edo ta ce a shirye take tsaf domin ba da tsaro a zaɓen gwamnan da za a yi a jihar ranar Asabar.
Mai magana da yawun rundunar, Moses J. Yamu, ya faɗa wa BBC cewa aƙalla jami'ansu 35,000 ne za su yi aikin gudanar da taro a ranar.
A gobe Asabar ne ake sa ran sama da mutum miliyan biyu da ke da katin zaɓe za su kaɗa ƙuri'ar zaɓen gwamna a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Jihar Edo na da ƙananan hukumomi 18 da rumfunan zaɓe 4,519.



