Najeriya ta ce za ta samar da lantarki ga ƴan ƙasar miliyan 17
Najeriya ta ce za ta samar da lantarki ga ƴan ƙasar miliyan 17
Hukumar samar da lantarki a yankunan karkara ta Najeriya ta ce cikin ƴan kwanaki masu zuwa ne za ta ƙaddamar da wani gagarumin aikin samar da lantarki ga ƴan Nijeriya sama da miliyan 17 a yankunan karkara.
Mallam Abba Abubakar Aliyu shi ne babban manajan Hukumar, ya shaida wa BBC cewa aikin wani ɓangare ne na wani gagarumin shirin Bankin Duniya da takwaransa Bankin Raya Ƙasashen Afirka na sama wa mutanen Afirka aƙalla miliyan 300 wutar lantarki nan da shekara ta 2030.



