Ko za a iya maye gurbin Daso a Kannywood?

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Ko za a iya maye gurbin Daso a Kannywood?

Fitacciyar tauraruwar Kannywood, Saratu Giɗaɗo ta cika shekara ɗaya da rasuwa, sai dai har yanzu ta bar abokan aiki da masu kallon fim cikin kewa.

Ta yi suna wurin barkwanci da kuma taka rawa ta ƙasaita a lokacin rayuwarta ta sana'ar fim ɗin Hausa.

BBC ta tattauna da ƙanwar marigayiyar, Zinaru Muhammad Giɗaɗo kan lokaci na ƙarshe na rayuwar tauraruwar da kuma yadda rayuwa ta kasance bayan rasuwarta.