...Daga Bakin Mai Ita tare da Kilishi ta Labarina

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
...Daga Bakin Mai Ita tare da Kilishi ta Labarina

Cikin shirinmu na wannan makon mun kawo muku hira da fitacciyar jarumar Kannywood da ke tashe a yanzu wato Hauwa Musa Adam da aka fi sani da Kilishi a cikin shirin Labarina mai dogon zango.

An haifi Hauwa a ƙauyen Dulum da ke garin Jos a jihar Plateau.

Bayan faɗan ƙabilanci da aka yi a garin Jos a 2002/2003 Hauwa Musa Adam ta daina zaman ƙauye inda ta koma cikin garin Jos domin ci gaba da rayuwa.

Jarumar - wadda ƴar ƙabilar Birom ce - ta ce kodayake ba ta yi karatu mai zurfi ba, ta yi firamare da sakandire, sai kuma ilimin zama da jama'a da ta samu.

Kilishi ta ce tun tana Furamare take da sha'awar shiga harkar film.

Ta ce bayan aurenta ya mutu ne ta sabunta sha'awarta ta shiga harkar film.

Film na farko da jarumar ta fito a ciki shi ne 'Babbar Ƙasa' wanda suka ɗauka tare da jaruma Marigayiya Saratu Giɗaɗo.

Hauwa Musa Adam ta ce fina-finan da ta yi sun haɗa da Babbar Ƙasa da Birgima Bincike da Gida Bakwai da sauransu.

Amma ta ce babban film ɗin da ya zama ginshiƙinta shi ne Labarina, sannan ta fito a fina-finai masu dogon zango irinsu su Jamilun Jidda da Allura Cikin Ruwa da Gidan Sauta da Za mu Zauna.

'Rashin aure ne ya kawo ni film'

Kilishi ta ce babu abin da take buƙata a rayuwarta kamar aure.

''Ai rashin abinda nake so ne ya kawoni film, domin duk duniya babu abin da nake so kamar rayuwar aure'', in ji ta.

Jarumar ta ce babban abin da faranta mata rai shi ne ta faranta wa abokan iyayenta, kasancewa ita nata iyayen sun mutu.

Hauwa Musa Adam ta ce abin da ke baƙanta mata rai shi ne yadda mutane ke yawan tambayarta yaushe za ta yi aure.

'An taɓa dukana saboda ina fitowa a muguwa'

Kilishi wadda galibi ke taka rawar ''muguwa'' a fina-finanta ta ce hakan na sanya ta fuskantar barazana ita da iyakanta.

"Akwai ranar da na fita cikin Adaidaita sahu, wasu matasa suka tare ni suka doddokeni harma suka farfasa adaidaitan da nake ciki'', in ji ta.

Sai dai ta ce daga baya sun samu fahimta da matasan bayan sun fahimci abin da take yi shiri ne ba halinta na gaskiya ba.

Kilishi ta ce babban abin da ke zame mata ƙalubale a aiki shi ne yadda ake sanya su zanja tufafi a lokacin ɗaukar film.

Kilishi ta ce abinci da ya fi so shi ne nau'ikan abincin gargajiya irin su tuwo da dambu ko ɗanwake da sauransu.

'Burina shi ne in zama kamar Layla Othman'

Jarumar ta ce babban burinta shi ne ta zama kamar Layla Othman wajen hidimta wa al'umma.

''A kullum ina roƙon Allah ya ba ni damar da zan tallafa wa mutane masu buƙata'', in ji ta.

Ta kuma shawarci ƴan'uwanta jarumai su ji tsoron Allah su kuma kasnec masu kamun kai a duk abubuwan da suke.

Daukar Bidiyo: Fatawul Mohammed

Tacewa: Abba Auwalu