Taron sauyin yanayi na COP28: 'Ya kamata a saurare ni'
Taron sauyin yanayi na COP28: 'Ya kamata a saurare ni'
Sagarika Sriram mai shekara 18 da haihuwa na daga cikin matasa masu ƙarancin shekaru da ke halartar taron sauyin yanayi na COP28 a birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Tana cikin mata 100 da BBC ta zaɓo a matsayin waɗanda suka yi fice a 2023.
Ta ce duk haduwa domin tattauna matsalar sauyin yanayi na da muhimmanci amma aiwatar da ƙudurorin magance illolin sauyin shi ne abin da ya fi muhimmanci.



