Rijiyar da ta haura shekara dubu ɗaya a jihar Gombe

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Rijiyar da ta haura shekara dubu ɗaya a jihar Gombe

Rijiyar 'Buzurdalla' wata rijiya ce a garin Wawa da ke ƙaramar hukumar Funakaye ta jihar Gombe, arewacin Najeriya.

Tarihi daga mazauna garin ya nuna cewa ana amfani da rijiyar tun fiye da shekaru 1000 da suka gabata.

Dagacin garin na Wawa, Abubakar Sadik Lawal ya ce wata goɗiyar doki ce ta gano rijiyar.