Yadda tsananin yunwa ta tilastawa ɗalibai cin ƴaƴan itace domin su rayu a Tigray

Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
Yadda tsananin yunwa ta tilastawa ɗalibai cin ƴaƴan itace domin su rayu a Tigray

Wasu mutane sun ƙona wata makaranta a yankin Tigray, abin da ya sa koyarwa ya zama abu mai wahala.

Dalibai na fama da yunwa, ita kuma makarantar an lalata ta.

Shugaban makarantar, Yemane Teklay, ya ce abin da ya faru yana damunsa.

A cikin wata uku, fiye da yara 200,000 ne suka bar makaranta, waɗanda ba su bari ba kuma suna karatu cikin wahala.