Ambaliyar Maiduguri: Halin da asibitoci ke ciki bayan ambaliyar

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama
Ambaliyar Maiduguri: Halin da asibitoci ke ciki bayan ambaliyar

Asibitoci da ya kamata su zama wurin da jama'a za su samu lafiya, a birnin Maidugurin jihar Borno da ke Najeriya, asibitocin su ma sun fuskanci matsalar ambaliya.

Ambaliar da aka yi a ranar 10 ga watan Satumbar 2024 kusan dukkannin asibitocin da ke birnin na Maiduguri, inda aka mayar da marasa lafiya zuwa kan bene.

Wani abun fargaba ma shi ne yadda wasu sinadarai suka haɗe da ruwan wani abun da yake jefa fargaba a zukatan ƙwararru cewa cutuka ka iya yaɗuwa sakamakon cukudar ruwan da sinadarai.