Ku San Malamanku tare da Sheikh Isa Ali Pantami
A shirin Ku San Malamanku na wannan makon mun tattauna da Sheikh Isa Ali Pantami tsohon ministan sadarwa na Najeriya.
An haifi Sheikh Isa Ali Pantami a garin Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Shehin malamin ya ce ya fara karatun addini ne a wajen mahaifi da mahaifiyarsa.
Ya ce ya halarci makarantar furamare ta Pantami, daga nan ya zarce ƙaramar sakandiren horas da fasahohi ta Gombe, sai kuma babbar sakandiren Kimiyya ta Gombe.
Ya kuma karanta fannin fasahar zamani wato Computer Science a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
A jami'ar ne kuma ya samu digirinsa na biyu a dai fannin fasahar zamanin, sannan ya karanta fannin gudanarwar fasaha wato MBA Technology Management.
Daga nan ya je Birtaniya inda ya samu digirinsa na uku a fannin Fasahar zamani, wato Phd Computer Information System.
A shekarar 2019 tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa shi ministan sadarwa, muƙamin da ya riƙe har lokacin da Buhari ya sauka a 2023.
'Na yi karatu a wajen Sheikh Sudais'
Malamain ya ce daga cikin malaman da ya yi karatun addini a wajensu har da Sheikh Malam Abba Aji da ke Maiduguri, da Sheikh Sayyid Attawi shugaban jami'ar Azhar da ke Misra, da limamin harami Sheikh Abdurrahman Sudais.
Ya kuma ce ya yi karatu a wajen malaman addini na ciki da wajen Najeriya masu ɗimbin yawa.
'Karatun boko ya ƙara min fahimtar addini'
Sheikh Pantami ya ce karatun bokon da ya haɗa da na addini ya taimake shi matuƙa wajen ƙara fahimtar addini.
Saboda a cewarsa a lokuta da dama idan binciken kimiyya ya gano wani sabon abu, to sai ya ga cewa alqur'ani ya yi magana a kan wannan abun fiye da shekara dubu da suka gabata.
''Haƙiƙa wannan abu ya ƙara min fahimtar addini'', in ji Sheikh Pantami.
'Ɓangaren ilimin da na fi sha'awa'
Sheikh Isa Ali Pantami ya ce fannin ilimin da ya fi ɗanfaruwa shi, shi ne ilimin Alqur'ani, amma kuma hakan bai hana shi sha'awar fannin ilimin hadisai ba
Wasan ƙuruciya
Shehin malamin ya ce a lokacin da yake matashi, da lokacin ƙuruciyarsa ya yi wasan ƙwallon ƙafa sosai, saboda yadda yake da sha'awa da ɓangaren.
Ya kuma ce a lokacin da yake buga ƙwallo, ana ji da shi sosai a cikin fili, domin kuwa har kofi ya taɓa ɗauka lokacin yana makarantar furamare
'Abincin da na fi sha'awa'
Malamin addinin - wanda shi ne tsohon ministan sadarwa na Najeriya - ya ce abincin da ya fi sha'awa shi ne tuwo da miyar kuka, da ɗan wake.
A ɓangaren nama kuma Sheikh Pantami ya ce ya fi sha'awar naman zabuwa da na kaza da kuma kifi.
'Surar da na fi so'
Tsohon ministan ya ce surar da ya ke son karantawa ita ce suratul Iklas indai ta ɓangaren lada ne da sanin girman Allah.
In kuma a ɓangaren sanin darussa da gwagwarmayar rayuwa ne to ya fi son suratul Yusuf



