Matashiyar da ta rungumi harkar noma a Jigawa
Matashiyar da ta rungumi harkar noma a Jigawa
Fatima Yusuf Kaigama, wata matashiyar manomiya ce a jihar Jigawa da ke bai wa sama da mutum 30 aikin yi silar aikinta.
Ta shaida wa BBC yadda ta rungumi noma a matsayin hanyar dogaro da kai.
Fatima ta ce tana noman shinkafa da alƙama da kayan lambu irinsu salat da attaruhu da albasa a gonarta.
Ta ce ta gaji sana'ar noma da wajen kakanta da kuma mahaifinta, lamarin da ya sa ta samu sha'awar sana'ar.
Matashiyar ta ce ta karanta fannin aikin noma a jami'a, don haka tana da ilimin noma.
Ta ce sana'ar da take yi ya sa ba ta sha'awar aikin gwamnati, kodakuwa da ta samu aikin gwamnati ba za ta daina sana'ar noma ba.



