Ƙasashe nawa ne mata ba su taɓa mulka ba a duniya?
Ƙasashe nawa ne mata ba su taɓa mulka ba a duniya?
A faɗin duniya, shigar mata cikin siyasa na ƙaruwa a hankali a hankali, inda shigar mata siyasa ya fi samun tagomashi a ƙarshen ƙarni na 20 zuwa farkon ƙarni na 21.
A 2008, majalisar dokokin Rwanda ta zamo ta farko a duniya da ta zaɓi mace a matsayin shugabar masu rinjaye.
A yanzu, a ƙasashe uku ne kacal cikin 193 - wato Rwanda da Cuba da kuma Nicaragua - mata ke da rinjaye a majalisar dokoki.



