Abin da aka tattauna a taron raya yankin arewa maso yammacin Najeriya

Taron hukumar raya yankin arewa maso yammaci

Asalin hoton, @NWDCOfficialNg

Lokacin karatu: Minti 3

Hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a shiyyar arewa maso yammacin kasar na ci gaba da bayyana fatan su wajen ganin an shawo kan matsalolin da suka addabi yankin.

A kan haka ne Majalisar dokokin kasar ta shirya wani taro a Kaduna kan yadda za a tunkari ayyukan raya kasa na Hukumar Kula da ci gaban shiyyar wato Northwest Development Commission.

Kwamitin majalisa dattawa mai kula da Hukumar Bunkasa shiyyar arewa maso yamma dana bangaren majalisar wakilai nai suka shirya taron inda aka gayyato masana da suka gabatar da jawabi a kan irin matsaloli da ke addabar shiyyar da ma yadda za a magance su.

Wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron sun bayyana irin matsalolin da ke damun yankin arewa maso yamma da kuma hanyoyin da suke gani za a magance su.

Sai dai an yi taron ne ba tare da halartar ɗaya daga cikin gwamnonin yankin ba, sai dai suka turo wakilai, lamarin da ya sa wasu masana a wajen taron ke ganin rashin halartarsu ya rage wa taron armashi da kuma rashin tabbas ga manufar haɗuwa a tattauna kasancewar su ne shugabanni.

Matsaloli da dama ne aka tattauna, amma an fi bayar da fifiko kan waɗanda suka addabi yankin.

Tsaro

Majalisar dattawan Najeriya ta ce kalubalen tsaron da jihohin shiyyar arewa maso yamma ke fama da su su ne a kan gaba wanda majalisar ta ce su ne hukumar raya yankin za ta ba wa fifiko.

Sanata Babangida Hussaini, shugaban kwamitin majalisar dattawan Najeriya mai kula da hukumar ta raya yankin na arewa maso yamma, ya shaida wa BBC cewa, sai an kare rayuwa da dukiyar al'umma ne za a fara tunanin mai za a kawo musu na ci gaba kuma.

Ya ce," Tsaro ne kan gaba a kan abin da hukumar za ta fara ba wa fifiko, domin akwai jihohin yankin da ke fama da matsalar tsaron da ta ki ci taki cinyewa, wanda kuma ke kawo matsala wajen ci gaban al'ummar yankin, don haka dole sai an samar da hanyoyin da za a tabbatar da tsaron al'ummar shiyyar arewa maso yamma kafin a kawo musu ayyuka ci gaba." in ji shi.

Talauci

Talauci na daga cikin abubuwan da yankin arewa maso yammacin Najeriya ke fama da shi.

Yankin dai shi ne yankin da ya fi yawan al'umma a Najeriya, sannan kuma akwai abubuwan da suka sanya yankin ke fama da talauci kamar rashin tsaro da rashin aikin yi da kuma cin hanci da rashawa.

Farfesa Isa Ali Fantami, na daga cikin masanan da suka gabatar da kasida a wajen taro, ya bayar da shawarwarin da ya ke gani ya kamata shugabannin yankin su bi domin magance matsalolin da yankin ke fama da su.

Ya ce," Dole ne shugabannin yankin su fifita dan'adam, wato a gina al'ummar yankin ta hanyar ba su ilimi da tarbiyya da kuma sana'oi."

A shekarar 2024 ne aka samar da hukumar raya yankin arewa maso yammacin Najeriya da nufin bunkasa jihohi da ke shiyyar.

Jihohi bakwai ne ke karkashin wannan hukuma da suka hada da Kano da Kaduna da Katsina da Kebbi da Sokoto da Jigawa da kuma Zamfara.