...Daga Bakin Mai Ita tare da Zaidu na Gidan Badamasi

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
...Daga Bakin Mai Ita tare da Zaidu na Gidan Badamasi

A cikin shirin ...Daga Bakin Mai Ita da muke kawo muku a kowane mako, a yau mun kawo muku hira da Muhammad Aminu Shehu da aka fi sani da Mallam Zaidu na Gidan Badamasi.

Mallam Zaidu ya ce ya fara harkar film tun a 1997, amma sai a 1999 aka fara haska shi a fina-finan Hausa, kodayake ya ce sai a shekarar 2000 zuwa 2001 ya fara fice a masana'atar a lokacin da ake kiransa da Aminu Mirror.

Ya ce ya yi amintaka da tsohon jarumin Film marigayi Ahmad S Nuhu, da ya ce sun yi zumunci mai zurfi kafin Allah ya yi sama cikawa.

Ya ce Darakta film ɗin Gidan Badamasi ne ya ba shi matsayin Mallam Zaidu a ciki film ɗin, bayan ya burge shi a wani film.

Mallam Zaidu ya ce yana da mata uku da ƴaƴa 13, kuma abincin da ya fi so shi ne abincin da aka tuƙa da hannu.