Daga Bakin Mai Ita tare da Murja Mangu
Daga Bakin Mai Ita tare da Murja Mangu
Murjanatu Yusuf, wadda aka fi sani da Murja Mangu, 'yar fim ɗin Kannywood ce da ta daɗe ana damawa da ita a masana'antar.
Ta girma a garin Jos, inda ta yi firamare da sakandare a babban birnin na jihar Filato. Ta ce ta yi finafinai da dama.
Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan ya karɓi baƙuncinta, inda ta shaida wa BBC cewa akwai ɗanta da ba ya iya kallon wani fim da ta yi saboda rawar da ta taka a cikinsa.



