Bayern ta miƙa tayi kan Luis Diaz, Real za ta sanya Rodrygo a kasuwa

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich ta gabatar da tayin Yuro miliyan 52 (£44.7m) kan ɗan wasan Liverpool da Colombia Luis Diaz mai shekara 28. (Bild)
Real Madrid a shirye take ta bar ɗan wasan Brazil Rodrygo ya fice daga ƙungiyar a bazara, amma kulob ɗin zai bar wa ɗan wasan mai shekara 24 wanda ke son ci gaba da zama a Turai zaɓin yin hakan. (Fabrizio Romano)
Bayan da Real ta sha kashi a gasar cin kofin duniya, koci Xabi Alonso na son sayar da Rodrygo, tare da ɗan wasan tsakiya na Sifaniya Dani Ceballos, mai shekara 28, da ɗan wasan tsakiya na Morocco Brahim Diaz, mai shekara 25. (Fichajes).
Ƙungiyar ta Sifaniya na shirin ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan bayan Tottenham Hotspur Cristian Romero, mai shekara 27, wanda kuma ke jan hankalin abokiyar hamayyarta Atletico Madrid. (Fichajes)
Arsenal na da ƙwarin gwiwar cewa ɗan wasan Ingila na ƴan ƙasa da shekara 21 Ethan Nwaneri zai rattaba hannu kan sabon kwantaragi duk cewa ɗan wasan mai shekara 18 na jan hankalin Chelsea da kuma wasu ƙungiyoyi a Jamus. (Guardian)
Brentford ta sake yin watsi da tayin da Nottingham Forest ta gabatar kan ɗan wasan gaba Yoane Wissa, mai shekara 28. (The Athletic)
Liverpool a shirye ta ke ta fara tattaunawa kan neman ɗaukar ɗan wasan Eintracht Frankfurt Hugo Ekitike, mai shekara 23, duk da cewa ƙungiyar na buƙatar sallamar ɗan wasan gaban Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 26, kafin ta iya fara cinikin ɗan wasan na Faransa. (Givemesport)
Zawarcin da Arsenal ke yi wa ɗan wasan Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27, tangal-tangal saboda ƙungiyar ba ji komai daga ɓangaren Sporting batsawon kwanaki uku. (Abola)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Napoli ta dakatar da tattaunawar da ta ke yi da Galatasaray kan Victor Osimhen, mai shekara 26, saboda rashin cimma matsaya kan farashi. Ɗan wasan na Najeriya ya yi zaman aro a kulob ɗin na Turkiyya a kakar wasan da ta gabata. (Gianluca di marzio)
Sunderland na tattaunawa da ɗan wasan Ingila Romaine Mundle game da rattaba hannu kan sabon kwantiragi, yayin da ɗan wasan mai shekara 22 ke jan hankalin PSV Eindhoven. (Sky Sports).
Kocin Fenerbahce Jose Mourinho yana sha'awar ɗan wasan gaban Belgium Leandro Trossard, inda Arsenal ke shirin sayar da ɗan wasan mai shekara 30. (Fotospor)
Real Betis ta na da ƙwarin gwiwa a yunƙurinta na ɗaukar ɗan wasan Brazil Antonydaga Manchester United kan kwantiragin dindindin, duk da cewa sai ɗan wasan mai shekara 25 ya rage albashinsa kafin ya iya komawa ƙungiyar ta Sifaniya. (Sport)
Ɗan wasan gaban Ingila Jamie Vardy, mai shekara 38, yana jan hankalin tsohon kociyan West Brom Carlos Corberan, wanda yanzu shi ne kocin Valencia a gasar La Liga. (Givemesport)











