Abin da ya sa na fara tuƙa babur mai ƙafa uku duk da kasancewa ta mace

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Abin da ya sa na fara tuƙa babur mai ƙafa uku duk da kasancewa ta mace

"Har yanzu akwai wasu mata da ke tsoron hawa, suna cewa 'mace ma za ta iya? kada ta je ta kifar da mu'."

Amina Hassan, wadda ke sana'ar tuƙa babur mai ƙafa uku ta ce sukan fuskanci ƙalubale sosai ganin cewa ana yi wa tuƙin babur a matsayin sana'ar maza.

Amina na sana'ar tuƙa babur ɗin ne a Kano, ɗaya daga jihohin arewacin Najeriya da ake ƙyamar cakuɗuwar maza da mata, inda wata ƙungiya ta fito da shirin samar wa mata mafita, kasancewar 'A daidaita sahu' na daga cikin hanyar sufuri mafi shahara.