Ba mu yi wa kowa alƙawarin tikitin takarar shugaban ƙasa ba - SDP

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Ba mu yi wa kowa alƙawarin tikitin takarar shugaban ƙasa ba - SDP

Shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa, Alhaji Shehu Musa Gabam ya yi watsi da yunƙurin haɗaka tsakaninta da sauran jam'iyyun adawa da nufin tunkarar zaɓen 2027, sannan ya bayyana cewa babu wani mutum da aka yi wa alƙawarin samun tikitin takarar shugaban ƙasa.

Wannan na zuwa yayin da ake ganin tagomashin jam'iyyar ta SDP ya karu sakamakon sauya sheƙar da wasu manyan 'yansiyasa a ƙasar ke yi zuwa cikinta.