Masu mayafi da ke yaƙar mayaƙan al-Qaeda da al-Shabab a Somaliya

- Marubuci, Mary Harper
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa Editor, BBC World Service
Wasu mayaƙa da ba a yi tsammani ba na taimaka wa gwamnatin Somaliya a yaƙin da ta daɗe tana yi da ƙungiyar al-Shabab mai alaƙa da al-Qaeda - wadda ta kai harin tagwayen bam a babban birnin ƙasar Mogadishu a ƙarshen makon da ya gabata.
Hotunan mutanen da ke sanye da mayafai da takalmi silifa tare da bindiga rataye a wuyansu na cikin abubuwan da aka fi sani game da yaƙin na Somaliya. 'Yan Somaliya na kiran su da "ma'awiis".
Sukan sanya kaya marasa kala, su yi ado da kayan da ake ƙerawa daga Indonisiya.
Maza da dama kan saka su a matsayin kayan game-gari, yayin da wasu kan saka domin zuwa wuraren hira da yamma.
Yanzu masu mayafin ko kuma ma'awiisley, sun zama sabbin dakaru a yaƙin da zimmar kawo ƙarshensa bayan shekara 15 ana fafatawa.
Waɗannan mayaƙa sun fito ne akasari daga ƙauyukan manoma da ke zaune a ƙarƙashin al-Shabab, wadda ke iko da yanki babba a kudanci da tsakiyar Somaliya, kuma take saka dokoki masu tsauri kan mazauna yankin.

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa ƙungiyar masu iƙirarin jihadin na da masu tsaigunta masu bayanai a kowane lungu da saƙo da kuma yawan hukunta waɗanda suka bijire masu, wasu 'yan sa-kai sun fara nuna masu yatsa.
Yayin da fari ke mafi muni cikin shekara 40 ke ƙara ƙamari, mutane ba sa iya biyan al-Shabab harajin da take saka musu.
Kusan tan miliyan uku na amfanin gona ne ke lalacewa saboda ƙarancin ruwa, sannan kuma yanzu ba za su iya bai wa mayaƙan dabbobinsu ba kamar yadda ƙungiyar ke buƙata.
Sun daina ba da 'yan'yansu maza domin su yi aikatau a gonakin masu iƙirarin jihadin da kuma mata a matsayin bayinsu. Sun gaji kawai.
Ƙananan ƙungiyoyin manoma sun sha yunƙurin yaƙar al-Shababa 'yan shekarun nan, amma sai a murƙushe su.
Ma'awiisley sun fi yawa da tsari kuma sun fi yawan makamai da abinci da man fetur da gwamnati ke ba su.
Masu sharhi kan tsaro na cewa sojojin Somaliya ne aka sauya masu kaki.
"Ƴan bindigar na fuskantar hare-hare su kansu," a cewar Mohamed Mubarak, shugaban cibiyar harkokin tsaro da ke Mogadishu mai suna Hiraal.
"Idan abin ya karaɗe ƙasa baki ɗaya, ba na jin al-Shabab za ta tsira."
'Ba ma tsoro'

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Martanin da masu iƙirarin jihadin suka mayar ya nuna yadda suke tsoron ma'awiisley.
Sun ƙaddamar da ƙone-ƙonen gidaje da lalata rijiyoyi da kayayyakin kasuwanci da kashe 'yan kasuwar da ma dattijai na ƙabilar da mayaƙan ma'awiisley suka fito.
Cikin wani jawabi da ya yi wa ɗaliban da suka kammala sansanin horo na ƙungiyar a baya-bayan nan, kakakin al-Shabab Sheikh Ali Dheere ya bayyana ma'awiisley a matsayin "'yan fashi da masu fyaɗe da ke yawo a ƙasar kafin al-Shabab ta samu iko".
Sai dai Musa Idris Hassan, wani mamba a ƙungiyar mayaƙan ta ma'awiisley da ke tsakiyar Somaliya ya musanta wannan zargi.
"Mu makiyaya ne. Da ma can gwaraza ne. Mun zauna a ƙarƙashin 'yan bindigar tsawon lokaci saboda haka mun san komai game da su, ciki har da inda suke ɓuya.
"Za mu shiga kowane daji don gano su kuma mu yanka su gaba ɗaya. Ba ma tsoron al-Shabab ko wani mutum."
Ba mayaƙan ma'awiisley ne kaɗai ba. Suna dai cikin wani ɓangare muhimmi da gwamnati ke shirin kawo ƙarshen al-Shabab, ciki har da taimakon Amurka ta sama, da na dakarun ƙungiyar haɗin Afirka (AU), da 'yan ƙasar da suka samu horo a waje, da sojojin ƙasar, da dakarun jihohin ƙasar biyar.
"Ban taɓa ganin yadda ƙasashe ke nuna sha'awa ba game da yaƙi da al-Shabab," a cewar jagoran wannan yunƙuri Hussein Sheikh-Ali, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.
"Ma'awiisley na da muhimmanci a yaƙin nan. Suna ƙara mana ƙwarin gwiwa a yaƙar 'yan gwagwarmayar saboda sun fito ne daga yankin da suka mamaye.
"Suna taka muhimmiyar rawa ta hannyar ba da bayanan sirri da ke taimaka wa dakarunmu na musamman wajen zaƙulo 'yan bindigar. Yanzu mun kusa doke al-Shabab."
Haɗarin yaƙin ƙabila

Asalin hoton, AFP
Murƙushe al-Shabab kaɗai ba zai isa ba. Ƙalubalen shi ne na riƙe gari bayan kwato shi.
'Yan gwagwarmayar na da halin janyewa daga gari sannan su sake komawa bayan dakarun AU da na ƙasar sun janye.
Idan tana so ta yi nasara a yaƙin, gwamnati na buƙatar ta maye gurbin tsarin mulki da zamantakewa da al-Shabab ta kafa, ciki har da 'yan sanda da kotuna da tsarin haraji da makarantu da cibiyoyin lafiya.
Haka nan, Mista Mubarak ya gargaɗi gwamnati cewa dole ne ta san yadda za ta yi da mayaƙan ma'awiisley, waɗanda ya ce za su iya zama matsala.
An ƙwace garuruwa da yawa a baya-bayan nan. Yunƙurin haɗa ƙarfi da gwamnati wajen katse hanyoyin samun kuɗi ga ƙungiyar da kuma daƙile koyarwarsu, hakan ka iya zama mafita mai kyau, ko kuma kawo ƙarshen ƙungiyar baki ɗaya.











