...Daga Bakin Mai Ita tare da Marigayi Aminu S Bono
Daga Bakin Mai Ita, shiri ne na BBC Hausa da ke kawo maku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsu zalla.
A wannan mako, muna sake gabatar muku da tattaunawar da muka yi da fitaccen darakta a Kannywood Aminu S Bono, wanda Allah ya yi masa rasuwa ranar Litinin 20 ga watan Nuwamba. Cikakken sunansa Aminu Suraj Bono.
Cikin wannan hira da muka yi da shi a kashi na 108, marigayin ya fada mana cewa an haife shi ne a unguwar Dandago da ke tsakiyar birnin Kano.
Aminu S Bono ya ce ya fara karatu ne a Firamaren Dandago Special kafin ya wuce zuwa GSS Gwale.
Ya ce ya shiga masana'antar Kannywood a wajen 1999 a unguwarsu ta Dandago, wadda tana daya daga cikin cibiyoyin harkar fina-finan Hausa na zamani.
Wani abin arashi da Aminu S Bono ya shaida wa BBC a wannan hira, shi ne batun rasuwar yayansa Nura, wanda ya ce yana daya daga cikin abubuwan tashin hankali da ya tsinci kansa a tsawon rayuwarsa.
Daraktan ya ce babbar tambayar da aka fi yi masa, ita ce "Don Allah za ka sa ni a fim?"
Daga cikin fitattun fina-finan Darakta Aminu S Bono, akwai Ruhin Mijina da Kawayen Amarya da Agola da Zamantakewa da kuma Na Hauwa



