An gano tarkacen jirgin da ya ɓata a ƙarƙashin teku

Asalin hoton, Reuters
An gano tarkace a binciken da ake yi na Titan, jirgin da ke tafiya a ƙarƙashin teku da ya ɓace, kamar yadda aka ba da rahoton a ciki har da wani sashen wajen jirgin.
Ƙwararren mai ninƙaya David Mearns ya faɗa wa BBC shugaban ƙungiyar masu tafiye-tafiyen binciken ƙasa na Explorers Club - wanda ke da alaƙa da ƙwararrun masu ninƙaya - ya ce tarkace ya ƙunshi "wani faifan sauka a dandamali da kuma wata kariyar baya daga jirgin ƙarƙashin tekun".
Dakarun Tsaron Gaɓar Tekun Amurka tun da farko sun ce an gano "wani fili mai tarkace".
Yanzu ana ci gaba da bin ƙwaƙƙwafi.
Wata na'urar binciken ƙarƙashin teku da ake sarrafawa daga nesa ce ta hango tarkacen a kusa da karikicen jirgin ruwan Titanic.
Biyu daga cikin mutum biyar da ke cikin jirgin, akwai Hamish Harding wnai ɗan kasuwan Burtaniya da Bafaranshe mai tafiye-tafiyen bincike Paul-Henri Nargeolet, dukkansu wakilai ne na ƙungiyar Explorer's Club ma sansani a Amurka.
Jirgin ruwan ƙarƙashin tekun mai suna Titan ya ɓata ne a wani wuri mai nisa a cikin Tekun Arewacin Atalantika ranar Lahadi ɗauke da iskar oksijin ta tsawon kwana huɗu da mutum biyar a ciki.
Na biyar ɗin shi ne Paul-Henry Nargeolet, tsohon sojan ninƙayar Faransa ɗan shekara 77 da ya yi fice wajen tafiye-tafiyen binciken ƙasa.
Yayin wani taron manema labarai ranar Alhamis, Rear Admiral John Mauger na Rundunar Tsaron Gaɓar Tekun Amurka ya ce an yi imani tarkacen suna da kama da sassan jirgin da ke tafiyar ƙarƙashin tekun.














