Al-Shabab ta ce ta kame wani otal a Somalia

Asalin hoton, OTHERS
Kungiyar al-Shabab ta masu ikirarin jihadi ta ce ta kame iko da wani babban otal da ke kusa da babban birnin Somalia, Mogadishu.
'Yan-sanda sun ce maharan sun tayar da bama-bamai biyu a kofar otal din kafin su kutsa cikin ginin su bude wuta.
A wata sanarwa da 'yan kungiyar suka fitar sun ce su ke da iko da gaba dayan ginin a yanzu kuma za su harbe duk wanda ke ciki.
An ce otal din, Hayat, fitaccen wuri ne da ma'aikatan gwamnatin tarayyar kasar ke haduwa
Shugaban hukumar ayyukan motocin daukar marassa lafiya a birnin na Mogadishu, Abdikadir Abdirahman, ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an raunata mutum tara a otal din, wadanda aka kwashe a lokacin harin.
Wasu hotuna da ba a kai ga tantance sahihancinsu ba na ta yawo a shafukan intanet, da ke nuna hayaki na ta tashi daga otal din yayin da ake jin ihu da kara mai karfin gaske da fashewar abubuwa.

Asalin hoton, HAYAT HOTEL
Wani jami'in 'yan-sanda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a wata sanarwa cewa, an kai harin ne da bama-bamai da aka dana a motoci biyu.
Daya ya tarwatsa shingen shiga otal din dayan kuma ya tarwatsa kofar otal din .
Kungiyar al-Shabab, mai alaka da al-Qaeda, ta dade tana yaki da gwamnatin Somalia.
Kungiyar ke da iko da yawancin sassan kudanci da tsakiyar kasar ta Somalia,, kuma ta samu damar nuna tasirin ikonta a yankunan da ke karkashin ikon gwamnatin kasar a Mogadishu.
A 'yan makonnin nan mayakan da ke da alaka da kungiyar sun rika kai hare-hare a kan yankunan da ke kan iyakar Somaliar da Habasha, abin da ya sa fargaba da damuwa kan irin sabbin dabarun da kungiyar ta bullo da su.
Wannan hari da aka kai otal din shi ne na farko da al-Shabab din ta kai a babban birnin na Somalia tun da aka zabi sabon shugaban kasar, Hassan Sheikh Mohamud, a watan Mayu.










