Yadda mutane ke shan wahalar sufuri a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya

Bayanan bidiyo, Yadda mutane ke shan wahalar sufuri a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya
Yadda mutane ke shan wahalar sufuri a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ya kasance daya daga cikin biranen kasar da ke da mazauna da yawa wadanda akasarinsu ma'aikata ne.

To sai dai kuma matsalar da wasu da ke aiki a birnin ke fuskanta itace ta sufuri, domin za'a iya cewa tsarin sufuri da birnin ke da shi a baya ya ruguje.

Wasu ma'aikata dayawa a Abuja ba a kwaryar birnin suke zama ba kuma wasu daga cikinsu ba su da ababen hawa.

Wannan ne ke tilasta musu bin motocin kasuwa wadanda akasari ke cika makil tare da zagaye wasu unguwanni kamun su sauke dukkan fasinjojinsu.

Batun matsalar sufuri shi ne rahotonmu na karshe daga cikin jerin rahotanni da muka fara kawo muku kan rayuwa a Abuja tun ranar Talata 28 ga watan Yuni.

Kuma a cikin bidiyon mu na yau Juma'a, mun tattauna da wasu ma'aikata wadanda suka bayyana irin wahalar da suke sha kafun su fito wajen aiki ko kuma komawa gida.

Ita ma hukumar da ke kula da birnin tarayyar Najeriya FCDA ta amince akwai matsalar ta sufuri.

Shugabanta Shehu Hadi Ahmad ya ce suna sane da matsalar kuma abun babu dadi.

"Mun sani akwai matsalar zirga-zirga, babu abun hawa a gwamnatance kamar Bas-bas da kuma layin dogo, akwai matsalar cinkoso" in ji Shehu Hadi.

Ya kara da cewa "matsalar cinkoso tana son zama kamar anyi gudun gara a Lagos kuma an tarar da zago a Abuja domin daya daga cikin dalilan da suka saka aka dawo da birnin tarayya Abuja daga Lagos shi ne cinkoso".