Yadda aka kafa Abuja babban birnin tarayyar Najeriya
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Abuja babban birnin tarayyar Najeriya na daya daga cikin birane wadanda suka fi bunkasa a nahiyar Afirka.
An tsara tare da gina birnin Abuja ne a wani tankamemen yanki da aka debo daga wasu jihohi na tsakiyar kasar.
Wannan ya sha bam-bam ne da sauran biranen kasar wadanda suka kafu shekaru aru-aru da suka gabata ba.
An samar da birnin Abuja ne domin ya maye gurbin Lagos a matsayin babban birnin Najeriya.
Daga yau Talata BBC Hausa za ta fara gabatar muku jerin bidiyo kan babban birnin na Najeriya Abuja.
Bidiyonmu na yau ya mayar da hankali ne kan yadda aka samo birnin Abuja.