Yadda ake halasta kudin haram ta hanyar dillancin gidaje a Abuja
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, na daga cikin manyan biranen kasar da harkar ginawa da kuma sayarda gidaje ke cin kudi mai dumbin yawa.
A birnin ne aka fi samun kamfanoni da ke harkar gine-gine bayan jihar Lagos cibiyar kasuwancin kasar.
A ci gaba da kawo muku rahotanni kan rayuwa a birnin, yau Alhamis bidiyonmu na uku ya mayarda hankali ne kan yadda ake samun maka-makan gidaje da babu kowa cikinsu a birnin.
Hukumomi a Najeriya na cewa wasu mutane da ke wawurar kudaden gwamnati na fakewa da gina gidaje domin halsta kudin da suka sace.
A wani bayani da shugaban hukumar da ke yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC Abdulrasheed Bawa yayi, ya ce "idan da za a magance badakalar da ke cikin harkar samar da gidaje a Najeriya, to kuwa da za'a samu nasara matuka wajen rage yadda mutane ke halasta kudin haram."
Ita ma Kungiyar da ke sanya ido kan ayyukan majalisa a Najeriya CISLAC ta ce tayi bincike kan badakalar mallakar gidaje ba bisa ka'ida ba.
Shugaban kungiyar, Auwal Musa Rafsanjani ya ce " bincikenmu ya nuna cewa manya manyan ma'aikatu su na mallakar gidaje da gonaki da shaguna da filaye fiye da kudin da suke samu a matsayinsu na ma'aikatu.
An fi samun irin wadannan gidaje da filaye da kuma shaguna a biranen Abuja da Lagos da Kaduna da Fatakwal da kuma Kano in ji Rafsanjani.



