Ku San Malamanku tare da Adam Muhammed Ardo

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama don kallon bidiyon
Ku San Malamanku tare da Adam Muhammed Ardo

An haifi Mallam Adam Muhammed Ardo a 1970 a garin Wuro Dogo da ke cikin karamar hukumar Lau na jihar Taraba.

Ya fara karatu a makarantar Firamare ta Mafindi da ke cikin birnin Jalingo. Bayan nan ya tafi zuwa Government Teachers College.

Daga bisani ne kuma ya zarce zuwa Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya karanci fannin inshora.

Mallam Adam tare da wasu mutane sun buɗe wata mu'assasa mai suna Al'Rayyan Islamic Foundation a Minna, babban birnin jihar Neja, inda suka yi ta gudanar da harkokin da'awar addinin musulunci da karantarwa da sauransu.

Daga nan ne ya samu gurbin karo karatu inda ya tafi zuwa Jami'ar Musulunci ta Madina, inda ya karanci fannin Larabci. Bayan ya gama, sai ya sake yin digiri a fannin Shari'a a dai wanna Jami'a.

Ya ce an fi yi masa tambayoyin kan matsaloli da suka shafi mata da maza da kuma saɓani tsakanin iyaye da ƴaƴansu.