'Ba za a bar mu a baya ba a fannin noma'
'Ba za a bar mu a baya ba a fannin noma'
Wata manomiyar lambu a birnin Kaduna, ta ce bai kamata rikicin 'yan fashin daji ya hana al'ummar Najeriya noma abin da za su ci ba. Saboda in ji ta, "muna iya amfani da gidajenmu mu yi noma".
Adama Iliyasu Musa ta ce noma ba sana'ar wani jinsi guda ɗaya ba ne kawai. Mata ma suna iya yin noma saboda ba maza ne kawai suke cin abinci ba.
Matashiyar matar auren mai Gidan Gonar Gudulley ta ce burinta shi ne a ce da lambunta tana ba da gudunmawa wajen ciyar da al'ummar Najeriya.
Ta ce tana amfani da salon noma mai ɗorewa a lambunta, inda take amfani da tsirrai kamar darbejiya da feshin borkono wajen bunƙasa 'ya'yan itatuwa da kayan miyan da take nomawa, da kuma kashe ƙwari masu ɓarna a gona.



