Ƙishirwa na kashe 'yan Sudan ta Kudu saboda gaurayar ruwa da fetur

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Ƙishirwa na kashe 'yan Sudan ta Kudu saboda gaurayar ruwa da fetur

Gurɓacewar muhalli babbar matsala ce da ke tagayyara sassan duniya, musamman a nahiyar Afirka.

Al'ummomin da ke zaune a yankunan da ke da albarkatun man fetur sun daɗe suna kokawa kan yadda haƙar albarkatun man ke lalata ruwan sha, da hana su kamun kifi, da sauran wasu harkoki.

Irin wannan yanayin ne wata al'umma a ƙasar Sudan ta Kudu - ƙasa mafi sabunta a duniya - ta tsinci kanta, inda wasu ke mutuwa saboda ƙishirwa.