Ranar ruwa ta duniya: 'Mun gina rijiyoyin burtsatse kusan 2000 a ƙauyuka'

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallon bidiyo
Ranar ruwa ta duniya: 'Mun gina rijiyoyin burtsatse kusan 2000 a ƙauyuka'

Albarkacin Ranar Ruwa ta Duniya, Muhammad Mustafa, Shugaban Gidauniyar Water the Needy mai gina burtsatse kyauta a kauyuka ya bayyana mana yadda ya jagoranci gina burtsatse kusan 2,000.

Muhammad ya bayyana mana yadda suke gudanar da ayyukansu da kuma girman matsalar rashin ruwa a yankunan karkara a Najeriya.