Manyan mu'ujizozin haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W)
Manyan mu'ujizozin haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W)
A rana irin ta yau ta 12 ga watan Rabi'ul Awwal a duk shekara ne miliyoyin Musulmi a faɗin duniya ke bikin murnar zagayowar ranar da aka haifi Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Bisa maganganu mafi rinjaye, an haifi Annabin Muhammad (SAW) ne ranar Litinin a shekarar 570 a birnin Makka da ke Saudiyya.
Albarkacin zagowar ranar Mauludi, Malam Bashir Sheikh Tijjani Zangon Barebari ya faɗi abubuwan al'ajabi da suka faru a lokacin haihuwar fiyayyen halitta.
Tace hoto - Abba Auwalu



