Matar da ke bayar da hayar dabbobi don zuwa biki ko suna
Matar da ke bayar da hayar dabbobi don zuwa biki ko suna
Andrea Diaz ƴar Peru ta fara kasuwancin bayar da hayar wata dabba mai suna alpacas a yayin biki ko suna.
Sana'ar ta sa ta shahara har ma ta ajiye aikinta da take yi a Virginia da ke Amurka. Kamfaninta mai suna My Pet Alpaca ya fara ne da dabbobin alpaca biyu kacal, a yanzu kuma tana da 14.



