Hanyoyi biyar da aka fi samun hatsarin mota a Najeriya

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Hanyoyi biyar da aka fi samun hatsarin mota a Najeriya

Najeriya ƙasa ce mai girman gaske da kuma yawan al'umma, lamarin da ya sanya take buƙatar hanyoyin da za su riƙa sada al'ummunta daga wani ɓangare zuwa wani.

Duk da cewa akwai hanyoyin sufuri da dama, kamar jirgin sama, da jirgin ƙasa da kuma jiragen ruwa, amma yawancin al'umma a Najeriyar sun fi amfani ne da motoci domin zirga-zirga daga wuri zuwa wani.

Sai da tafiya ta mota na da nasa matsalolin a ƙasar, musamman ta ɓangareen ingancin hanyoyi da kuma tsaro. Ga wasu hanyoyi biyar da aka fi samun haɗura a Najeriya.