Gwamnan Kano ya naɗa sarakunan Gaya, Ƙaraye, Rano masu daraja ta biyu

Asalin hoton, KNSG
Gwamnan Kano a arewacin Najeriya, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin sarakuna uku masu daraja ta biyu a jihar.
Sanarwar da daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Bature, ya fitar ta ce sarakunan da aka amince da naɗa su sun haɗa da Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin sarkin Karaye, da Muhammad Isa Umar, a matsayin sarkin Rano da kuma Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin sarkin Gaya.
Sanarwar ta ƙara da cewa naɗin sabbin sarakunan ya fara aiki nan take.
Hakan na nufin gwamnan ya mayar da Aliyu Ibrahim Abdulkadir kan karagarsa ta sarkin Gaya bayan sauke shi sakamakon soke dokar masarautu ta 2019 da majalisar dokokin jihar ta yi. Sai dai wannan karon a matsayin mai daraja ta biyu.
A bisa tanadin sabuwar dokar ƙananan masarautu da gwamnan ya sanya wa hannu, masarautar Rano ta ƙunshi ƙananan hukumomin Rano da Kibiya da kuma Bunkure.
Masarautar Gaya kuma ta ƙunshi ƙananan hukumomin Gaya da Albasu da kuma Ajingi, yayin da kuma masarautar Ƙaraye da ta ƙunshi Ƙaraye da Rogo.
Gwamna Abba Ƙabir ya yi bayanin cewa sabbin sarakunan masu daraja ta biyu za su kasance ƙarƙashin masarautar Kano mai daraja ta ɗaya tare da tallafa wa sarkin wajen tafiyar da harkokin mulki a masarautun nasu.
A ranar Talata ne gwamnan na Kano ya sanya hannu kan sabuwar dokar da ta mayar da masarautun uku masu daraja ta biyu bayan soke dokar da ta ba su daraja ta ɗaya tun a watan Mayu.
Gwamnan ya amince da dokar ne bayan majalisar jihar ta yi wa dokar karatu na biyu da na uku yayin zamanta na ranar Talata.
Gwamnatin jihar ta kuma ce an yi wa dokar kwaskwarima ne domin farfaɗo da haƙiƙanin al'adun jama'ar jihar.
Wannan ya zo ne bayan hukuncin wata babbar kotun jihar da ta umarci sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu da dokar masarautun Kano ta 2020 ta kafa, da su daina ayyana kansu a matsayin sarakai.










