Abin da ƴan Gabon ke cewa kan naɗa soja a matsayin sabon shugaban ƙasa

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Abin da ƴan Gabon ke cewa kan naɗa soja a matsayin sabon shugaban ƙasa

Cincirindon fararen hular da suka yi ta sowa ne suka halarci taron rantsar da sabon shugaban mulkin sojan, Janar Brice Nguema.

Mutane da dama da suka zaƙu da ganin sauyi ne, suka yi maraba da juyin mulkin.

Sai dai wasu sun ce mulkin Janar Nguema, zai kasance wani ci gaba ne kawai na daular mulkin gidan Bongo mai shekara 55.

Sabon shugaban ƙasar Gabon, Janar Brice Nguema

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sabon shugaban ƙasar Gabon, Janar Brice Nguema