Shirye-shiryen Mahangar Zamani da suka fi shahara a shekarar 2023
Shirye-shiryen Mahangar Zamani da suka fi shahara a shekarar 2023
Kun tuna tattaunawarmu da Laila Ali Othman kan yadda matan da aurensu ya mutu za su shawo kan kalubalen rayuwa da wadda muka yi da Mista 442 kan zaman shi a gidan yarin Jamhuriyar Nijar?
Wadannan na daga cikin shirye-shiryen Mahangar Zamani da suka fi tayar da kura a 2023.
Gaba daya a shekarar da ke ficewa mun gabatar da shirye-shirye 24 na Mahangar Zamani, kuma a cikin wannan bidiyo mun tuno muku wasu da suka fi jan hankalin masu kallo.



